Kan Malaman Izala Ya Rabu A Kan Buhari Da Atiku




A karshen makon jiya ne Kungiyar Izala a Najeriya ta bukaci mabiyanta da su zabi Shugaba Muhammadu Buhari, amma wani jigo a kungiyar Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya ce shi Atiku zai zaba.
Sabanin matakin da kungiyar ta dauka, Sheikh Rigachikun ya bayyana alkiblarsa karara cewa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne zabinsa a 2019. Saboda “yadda yake yi wa addini hidima,” a cewarsa.
Sai dai Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, “ya kamata a yi saitin al’ummar Musulmi kan abin da ya kamata.”
Har ila yau, akwai Sheikh Ahmad Gumi wanda ya kwashe lokaci mai tsawo yana sukar manufofin Shugaba Buhari.
Kuma a lokuta da dama cikin karatunsa yana bayyana rashin goyon bayansa ga takarar Shugaba Buhari a 2019.
Sai dai bai fito karara ya ce a zabi Atiku Abubakar a zaben 2019.
Atiku

Hakkin mallakar hotoTWITTER/@ATIKU
Image captionSheikh yana cikin mutanen da suka sulhunta Atiku da Obasanjo a watan Oktoban 2018
Amma kuma yana cikin mutanen da suka sulhunta Atikun da tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo wanda ya yi aiki a karkashinsa.

No comments

Powered by Blogger.