Kannywood: Shekara 10 Kenan Da Auren Sani Danja Shida Matar Sa Mansura Isah (See Photos)



Shahararren dan wasan Kannywood Sani Danja tare da tsohuwar tauraruwar Kannywood Mansura Isah sun yi bikin cikar shekarunsu 10 da aure a ranar Alhamis 13 ga watan Yuli.

A shekarar 2007 ne Danja ya angwance da Mansura Isa, kuma cikin ikon Allah, Allah ya azurtasu da yaya 4, mace daya da maza 3.



Babbar yarsu sunanta Khadijatul Iman, sai Khalifa Sani, Yakubu da kuma Yusuf, kamar yadda majiyar HAUSATOP.com, jaridar Rariya ta ruwaito.

A yanzu haka dai Sani Danja ya shahara ba’a fannin wasannin Kannywood ba kadai, har ma da fannin wake wake, tallace tallace da kuma fina finan Turanci.

Ga sauran hotunan a nan:




No comments

Powered by Blogger.