An Gano Masu Satar Shiga Runbun Ajiye Bayanan Jama’a A Facebook




Hukumar lura da aiyyukan kanfanoni na Birtaniya tana neman izinin chaje ofishin kanfanin “Cambridge Analytica” sakamakon bayana da aka samu na cewa, kanfanin ta samu shiga runbun bayanan masu amfani da Facebook fiye da Miliyan 50 million. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan majalisa a Amurka da kasashen Turai suka nemi sanin yadda wannan kanfanin da ta yi aiki dsa ofishin shugaban kasar Amurka Donal Trump a lokacin zabe ta samu daman shiga runbun bayanan jama’a.
A Amurka,’yan majalisa sun gauyaci shugaban kanfanin Facebook Mark Zuckerberg domin bayar da shaida a gaban ta. Hukumar Facebook ta bayyana cewa, ta yi hayan kwararen kanfanin binciken nan mai suna Stroz Friedberg domin gudanar da binciken kwakwaf na ko kanfanin Cambridge Analytica na rike da wasu bayanan jama’a zua yanzu. “Masu bincike daga Stroz Friedberg sun gudanar da bincike a ofishin Cambridge Analytica dake Landan da yammacin nan” “Ofishin watsa labarai na Birtaniya ya bukaci a sanar da bayar da takardar binciken kanfanin Stroz Friedberg domin gano gasikiyar lamarin” Kanfanin Facebook tayi asarar hanun jari kasha 7.0 ranar Litinin abin day a kawar da fiye da Dala Biliyan 40 a kasuwar jari sabosa masu zuba jari na fargabar cewa, wannan dokar zai iya bata sunan kanfain a idon duniya musamman masu hakar zuba jari.
“Lamarin fallasar ya fito fili a kan yadda Facebook ta kasa kare bayanan mutane, abin kuma ba zai yi wa Facebook kyau ba” inji Frank Paskuale, malami a jam’ar Maryland kuma Farfesa a harkar sharia wanda ya yi dogon rubutu a kan badakalar Silicon Balley. Haka kuma wani majiya ta shaida mana cewa, ranar Litinin wani shugaban bangaren tsaro na kanfanin Facebook ya shiurya barin aiki saboda rashin jituwar da ta tsakanin shi da saiuran masu gudanar da kanfanin a kan tsarre-tsaren sun a tattalin bayanan mutane. Daman shi yana da ra’ayin kawo karshen zargin da ake yinwa facebook na barin kasar Rasha ta yi kanekane a farfajiyar Facebook a lokacin zaben kaar Amurka, a zaben day a gudana a shekarar day a gabata.
Gidan jaridar c eta fara bayar da labarin barin aikin na jam’in amma facebook  ta ki ta ce komai da aka nemi bayanin ta. A wani sako twiter day a aika, Stamos bai karyata batun tafiyarsa ba amma y ace, “Duk da raderadin da ake yin a tafiya ta, ina nan ina gudanar da aiki na a kanfanmin Facebook sai dai lallai aikin da nake gudanarwa ya canza” Wanna badakalar Cambridge Analytica ya zama babbar kalubale ga mutuncin kanfaninfacebook dukk day a riga ya fadi sakamakon batun kasar Rasha, in da ake zargin kaaar Rasha ta yinamfani da facebook wajen fitar da labaran karya kafin da bayan zabe da aka gudanar na shugaban kasa a kasar Amurka a shekara 2016.

No comments

Powered by Blogger.