So ko hauka: Wani saurayi ya kashe kansa saboda an kwace masa budurwa a Najeriya
Wani saurayi ya kashe kansa saboda an kwace masa budurwa a Najeriya
- Saurayin mai suna Prince dan jihar Bayelsa ne
- Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Wani matashin saurayi mai suna Prince dake a makarantar Sakandare ta jeka-ka-dawo ta Isaac Jasper Boro a karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa ya kashe kansa lokacin da ya gano wani saurayi ya kwace masa budurwa.
Shi dai Prince wanda akace dan asalin kauyen Kaiama ne a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma ance ya kwankwadi maganin kwari na fiya-fiya ne wanda sandiyyar haka ya margaya.
NAIJ.com ta samu cewa tuni dai iyalan mamacin suka rufe shi a ranar kamar yadda al'adar su ta tanada.
Wasu abokan mamacin da majiyar ta mu ta zanta da su sun nuna matukar kaduwar su da mutuwar ta sa sannan kuma suka yi takaicin dalilin da ya sa ya kashe kan sa.
'Yan sanda a jihar dai sun tabbatar da aukuwar lamarin.
A wani labarin kuma, Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Kwara sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawuratattun matsafa 'yan kungiyar asirin nan ta Badoo da suka addabi al'ummar jihar.
Majiyar mu ta Tribune, ta tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sandan sun cafke matsafan ne bayan wani samame da suka kai masu sakamakon bayanan sirri da suka samu daga wasu masu kishin kasa.

Post a Comment