Buhari Ya Cire Baffa Bichi Shugaban TETFund



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cire shugaban Asusun kula da karatun gaba da sakandare da bayar da tallafin karo karatu, wanda aka fi sani da TETFund, Dr Baffa Bichi.
Sanarwar da wani jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimi Mr Bem Goong ya fitar, ta ambato shugaban kasar na cewa an maye gurbin Dr Bichi da Farfesa Suleiman Bogoro, wanda a baya ya taba zaman shugaban asusun.
Sanarwar ba ta bayyana dalilin cire Dr Bichi daga kan mukaminsa ba, sai dai wasu masu sharhi na gani an cire shi ne saboda yadda ya tsunduma kansa cikin harkokin siyasar jihar Kano maimakon mayar da hankali a kan aikinsa.
Wasu mukarraban gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na ganin Dr Bichi na da hannu a rura wutar da ta taso lokacin da aka zargi Gwamna Ganduje da karbar cin hanci a wasu bidiyon da suka nuna shi yana cusa bandir-bandir na dala a aljihunsa.

A shekarar 2016 ne Dr Bichi ya maye gurbin Farfesa Bogoro a matsayin shugaban TetFund bayan an sauke Bogoron daga kan mukamin.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ne ya nada Farfesa Bogoro kan mukamin a 2014.
Yanzu dai za a iya cewa hannun bayar wa ne ya mika wa hannun karba.

Dr Baffa BichiHakkin mallakar hotoTETFUND
Image captionMasu sharhi na gani an cire Dr Baffa Bichi ne saboda yadda ya tsunduma kansa cikin harkokin siyasar jihar Kano maimakon mayar da hankali a kan aikinsa

No comments

Powered by Blogger.