Atiku Fa Kawai Bannatar Da Kudinsa Zai Yi A Kotu – Gwamnonin Jihar Neja Da Edo Suna Isgili
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, da gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a ranar Alhamis sun yiwa dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, isgili kan kokarin kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari a kotu.
Atiku ya lashi takobin cewa sai ya kwace kujeran shugaba Muhammadu Buhari a kotu bisa ga rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Febrairu, 2019.
Atiku ya lashi takobin cewa sai ya kwace kujeran shugaba Muhammadu Buhari a kotu bisa ga rashin amincewarsa da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Febrairu, 2019.
Obaseki da Bello sun bayyana cewa Atiku ba ya cikin hayyacinsa ne lokacin da yayi ikirarin cewa ya lallasa Buhari da kuri’u 1.6m a zaben.
Sun yi wannan magana ne a lokaci daban-daban ga manema labaran fadar shugaban kasa dake Abuja.
Obaseki yace: “Kun ji abinda aka ce, basu cikin hayyacinsu.”
Obaseki yace: “Kun ji abinda aka ce, basu cikin hayyacinsu.”
Shi kuma gwamnan jihar Neja ya baiwa Atiku shawara kada yayi asarar kudinsa saboda kotu ba zata bashi nasara ba.
Kana ya kara da cewa masu tunzura Atiku ya kalubalanci nasarar Buhari a kotu kudinsa kawai suke son ci.
Post a Comment