Kannywood: An Samu Sabon Jarumi Mai Kama Da Marigayi Ibro Sak


A yayin da masoya, yan uwa da kuma masu sha’awar kallon fina-finan Hausa ke ta jimami na rashin fitaccen jarumin nan na barkwanci watau Rabilu Musa IBRO, kwasam sai ga wani mai kama da shi ya bulla a masana’antar.






1xclusive ta samu labarin cewa yanzu haka dai matashin sabon jarumin Alasan Kanu ya samu damar fitowa a wani sabon fim mai suna ‘Jiki Magayi’ wanda a ciki kuma ya taka muhimmiyar rawa.

Idan ba’a manta ba dai Allah ya karbi ran marigayi Rabilu Musa Ibro ne kimanin fiye da shekara daya kenan bayan ya sha fama da gajeruwar rashin lafiya inda kuma har yanzu ba’samu wanda ya cike gibin sa ba.




No comments

Powered by Blogger.