Ni Kadai Ce Zan Iya Gyara Najeriya – Ezekwesili

Ni Kadai Ce Zan Iya Gyara Najeriya – Ezekwesili



Yar takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Allied Congress Party of Nigeria ( ACPN ), Farfesa Obiageli Ezekwesili a Jiya Alhamis, 17 ga watan Janairu tace ita ta canncanci jagorantar Najeriya zuwa tafarkin ci gaba.
Ta yi korafin cewa Najeriya bata samu shugabancin mai inganci ba da zai kai Najeriya inda take mafarkin zuwa.

Da take jawabi ga kungiyar yan wasa, matasa, dalibai, masu nakasa da wasu mata yan kasuwa a Arewa House, Kaduna, tsohuwar ministar ilimin ta ce ita kadai ce yar takarar da ta cancanci shugabancin Najeriya da fitar da ita daga matsalolin da take ciki.
Ta sha alwashin kawo ci gaba da inganta kasar zuwa matakin inganci.

No comments

Powered by Blogger.