Batun Tuhumar Gwaggo Babu Gaskiya A Ciki -Ganduje




Batun Tuhumar Matar Ganduje Babu Gaskiya A Ciki Sai Kazafi Da Yarfen Siyasa, Cewar Gwamnatin Kano
Martani Kan Maganar Shari’ah Tsakanin “Hope Development and Empowerment Foundation da EFCC da Ragowar Wadanda A Ke Kara, Mai Lamba CV/344/18 MT NO. M/887/18
Wani harhada zance kawai da a ka yi wai wata Babbar Kotu a Maitama, cikin birnin tarayya na Abuja, karkashin Mai Shari’ah Y. Halliru, kan abinda ya shafi matar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, wato Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, ba wani abu ba ne illa harigido da yamutsa zance da kuma karya bayyananniya.
Kawai wasu ‘yan siyasa ne ‘yan azarbabi da kuma irin mutanen nan da ba sa kunyar kitsa makirci da kinibibi, wadanda kullum burinsu kawai shine su dakusar da farin jinin da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ke samu daga jama’a. A dalilin jajircewa da ya yi ganin sai ya ciyar da wannan jiha ta mu gaba.

Magana ta gaskiya kawai ita ce, wannan Kotu da a ke maganarta sam sam ba ta fitar da wata Odar cewa wai a kama mai dakin gwamna Dakta Hafsat Umar Ganduje ba. Babu wannan maganar ma gaba daya.
Sannan ba kuma maganar cewa wai Kotu ta bayar da damar a kwace mata wasu abubuwan da ta mallaka ba, ko wadanda Mai Girma Gwamna ya mallaka ba. Gaba daya wannan zancen rudu ne ba shi da tushe balle makama.
Sannan kuma babu wata Oda daga wannan Kotu wacce wai ta nemi jam’iyyar APC da ta cire sunan Mai Girma Gwamna a matsayin dan takarar gwamna a jihar Kano, a zabe mai zuwa. Gaba daya babu wannan zancen. Ko kanshin gaskiya wannan zancen ba shi da shi.
Sa Hannu

Kwamishinan Shari’ah Na Jihar Kano
Barrister Ibrahim Mukhtar

No comments

Powered by Blogger.