Finally, Rahama Sadau ta Nemi Afuwa akan video da tayi da ClassiQ






Korarriyar Jarumar Finafinan Hausa Rahama Sadau ta fito fili karara ta nuna nadamar rungumar da ta yi wa wani mawakin ingausa mai suna Classiq. A faifan wakar, wacce ita ce ta farko da jarumar ta yi da harshen Turanci, an nunota tana rungume mawaki “Classiq” sannan tana kwanciya a jikinsa.



Jama’a da dama sun yi Allah-wadai da ita, sun kuma yi tir da abin da ta yi, yayin da wasu tsiraru suka yaba mata. Wanda hakan ya sanya kungiyar masu shirya Finafinan Hausa mai suna Moppan su ka dakatar da ita daga fim kwata-kwata a ranar 2, ga watan Oktoba 2016 shekara daya cif-cif kenan.

Yanzu haka dai jarumar ta nuna nadamar abin da ta yi, inda ta ba Gwamnan Kano da kuma Mai Martaba Sarki Kano hakuri a kan rungumar mawakin da ta yi. Jarumar ta kuma ce su gafarceta hakan ba zai taba sake faruwa ba a cewar ta. Sannan ta kuma sake ba masoyanta hakuri da dukkan wanda abin da ta yi ya batawa rai.

Korarriyar Jarumar ta bada hakurin ne a jiya talata a cikin wani shiri mai suna “Ku karkade kunnuwan ku” wanda ake gabatarwa a gidan rediyon Rahama da ke Kano. In dai ba ku manta ba wannan ba shi ne karo na farko da aka fara samun jarumar da aikata laifuka a masana’antar fim ba.

Masana da manzarta harkokin Finafinan Hausa sun zuba ido don ganin inda za a kwana dangane da korar na ta da aka yi tun da dai ta fito fili ta bada hakuri.

Sai dai ana ganin mutunci da kuma martabar masana’antar za ta ragu indai har su ka dawo da Rahama a harkar fim, don kuwa ana tunanin nan ba da dadewa ba, za su yi amai su lashe..

Mun dauko daga @kannywoodcelebrities

No comments

Powered by Blogger.