Mahaifiyar Marigayi Lil Ameer Tana Ma Masoyan Shi Godiya Game Da Addu’o’in Da Suke Yi Masa
Mahaifiyar marigayi Ameer Hassan wanda aka sani da lil-ameer ta ma masoyan shi godiya game da addu’o’i tare da fatan alheri da suke yi ma iyalin shi.
A wata hira ta musamman da tayi da Arewa24 Hajiya Maimuna Hassan tace bata taba sanin cewa danta ya kai matsayin da ya kai sai da ajalin shi ya taho.
“Masoyan Ameer ina maku godiya da goyon baya da kuka bamu, da wanda suke Nijeriya har da kasashen waje muna ganin sakonin ku, mun gode kuma Allah ya saka maku da alheri.
Bamu taba sanin Ameer yana da masoya sai da abun ya faru, mun gode muna muku godiya” tace.
playMarigayi tare da mahaifiyar shi
Mahaifiyar tace tana kewar marigayi tare da yaba halayyar shi na yaron kirki ne kuma mai nagartaccen halin ne kuma yana so mahahafiyar shi sosai.
Tayi kira ga sauran iyaye da su mara ma yaran su baya indai suna da burin yin waka ba wai su tilasta masu wani buri daban.
Marigayi ya rasu sanadiyar hatsarin da ya samu saman babur hanyar shi zuwa gida a garin Kano.
Allah ya jikan shi da rahama… Ameen.
Post a Comment