Kannywood: Har Yanzu Muna Yiwa Ibro Addu’a – Inji Sulaiman Bosho




Fitaccen jarumin barkwancin nan na fina-finan Hausa dake a masana’antar Kannywood mai suna Sulaiman Bosho dai na zaman daya daga cikin jerin wanda mutuwar jarumi marigayi Rabilu Musa Ibro ta fi daidaitawa a cikin masu sana’ar ta fim.



Mutuwar dai ta Alhaji Rabilu Musa Ibro ta razana jarumai masu tarin yawa sai dai amma jarumai irin su Sulaiman Bosho, Malam Dare, da Rab’u Daushe sune a sahun farko da za’a iya cewa sun fi kaduwa da mutuwar ta sa musamman idan aka yi la’akari da kusancin su.



NAIJ.com ta samu a cikin wata fira da aka yi a gidan Radion jihar Kano fitaccen Jarumin Sulaiman Bosho ya bayyana cewa har yanzu bai daina tunanin marigayi Ibro ba. duk ranar daya tuna shi sai yaji aransa kamar alokacin ya rasu.

A cewar shahararren jarumin da aka fi sani da Bosho: “Tabbas, mutuwar ibro ba zamu iya mantawa da itaba don kuwa haka har yanzu muna yi ma shi addu’a kuma muna fatan Allah yaji kan sa ya kuma kyautata tamu idan ta zo.”

No comments

Powered by Blogger.