Yanda Aliko Dangote Ya Zama Shahararen Mai Kudi A Afrika

Yanda Aliko Dangote Ya Samu Nasara A Kasuwancin Sa



Barkan Muda warhaka. Yau ina so in rubuta post akan Shaharraren mai kudin Afrika Da Yanda Ya Zama shaharraren Maikudin Afrika...

Kafin na rubuta post dinah nayi nazari sosai kuma na duba hirar da akayi dashi da kuma wasu jawabi a yanar Gizo daga nan na fito da nawa post din...

Ina fatan mai karatu zai samu abunda zai amfane shi a post dinah...
Zanyi Rubutunah a Takaice...

Aliko Dangote a haife shi a Garin Kano, Mahaifinsa Muhammad Dangote , Mahaifiyarsa Hajiya Mariya Sanusi Dantata .
Kamfanin Shi yana aiki a Nigeria da kasashe kamar su Benin Ethiopia,
Senegal,Cameroon ,Ghana, South Africa,Togo, Tanzania, and Zambia.
A watan february 2017 a kiyasta kadara takai dalar amurka US$12.5 bilyan...

Bari mu cigaba ina fatan kun fahimce wanda zanyi magana akai..

Kabi abunda kake so :
Aliko Dangote ya fada a hirar da akayi dashi yace ya a fannin kirkira da kuma kasuwancin tun yana yaro yake sha'awar hakan. " Ya ce zan iya tunawa tun ina makarantar primary nake siyan katon din alewa domin in samu kudi. Tun yana karami yake son kasuwanci.

Dangote ya nuna , yafi sauki ka zama mai nasara akan abunda kake so fiye da samun nasara akan abun da baka da ra'ayin shi..

Wasu lokutan basai mun sami nasara kamar Aliko Dangote ba amma bin abunda kake so zai kawo maka cikar burin a rayuwa. Karda ka bar matsalar rayuwa tasa ka canza zuwa abinda baka ra'ayi.

Fara koma mene ne a yau komai kankantar abun..

Kayi aiki da mutane masu ilmi :
Aiki tare da mutane masu ilmi zai baka damar samun shawarwari da ra'ayinsu wanda zai kawo maka cigaban kasuwancinka. Dangote yace yana daukan ma'aikata wanda suka fishi ilmi a kamfaninsa domin kawo cigaban Kamfanin sa.

A matsayin dan kasuwa karda kace sai dan uwa ko abokin ko ince dan kabilanka shine zaka dauka amatsayin dan aiki , Farko ka zabo wanda sun fara yin wani abu a fannin da suka kware kafin ka kawo su zuwa kasuwancin ka anan ne zaka samu Shawarwari da ra'ayi wanda zasu kawo cigaba Kamfaninka ko Kasuwanci ka..

Gina Samfurin Kaya [Brand] : Dangote Yace "
Domin Cigaban kasuwancinka ka bude Samfurin kaya kuma karda ka latata samfurin kayanka .

Yace samfurin sa na Dangote yasa ya wuce wanda yake gasa dasu kuma sabida baya siyar da jabun kaya sai masu kyau ne shi yasa koda zai kara bude wani kasuwanci mutane zasu siya sabida sun yarda kasuwanci shi..
Shiyasa koya karamin kasuwancinka yake ka bude samfurin kaya .

Taimaka Mutane ka :
Da zarar ka fara samun kudi a kasuwancinka ko kamfaninka toh saika fara taimakawa mutane ba ina ma'anar ka dunga baa kudi ta koyaya ba face ka taimaka ma garinka ko mutanen ka ta gina Makaranta , Asibiti .. Ka zamo kana bawa wanda suke bukata.. Dangote ya bada milyan 150 domin a magance Ebola.

Ka dunga bawa kanka lokaci hutawa : Lokuta dama da zaga da zarar dan kasuwa ya samu kudin zai komai baya hutawa amma yana da muhimmaci ka bawa kanka lokaci ta yanda zaka ziyarci abokanai da yan uwa .

Yace babu amfani kana da kudi amma baka bawa kanka lokacin hutawa domin taimakawa lafiyarka .

Yace yana kallan Kwallon Kafa na Arsenal da kuma Kallon Tashar Kasuwanci A TV..

Zan Tsaya Anan amma Dangote bai zama mai kudi ba saida ya bada lokacin,sonshi na kasuwanci,juriya da duk kokarin shi domin zama mutumin da yake a yau ..

Ina fatan Wannan Post din Ya Amfane ka Mai Karatu Zaka Iya Adding dinah a amatsayin aboki a facebook idan kana son abubuwa da zasu kawo cigaban ka

#Sadikdeveloper


No comments

Powered by Blogger.