A Ranar Asabar Shugaba Buhari Zai Ziyarce Kasar Poland




A gobe Asabar ne jirgin Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tashi Daga Birnin Tarayya Abuja zuwa Katowice Babban Birnin kasar Poland Inda zai Halarci Babban Taron (COP) a kan Sauyin Yanayi da karo na 24 a Karkashin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya game da Sauye-sauyen yanayi (UNFCCC) wanda za’a Gudanar Ranakun 2-4 na Disambar wannan Shekarar ta 2018.
Taron na COP24, wanda za a gudanar a Cibiyar Kasuwanci ta Duniya (MCK) da kuma filin jirgin ruwa na Spodek Arena a Katowice, Babban Birnin kasar Poland.

A Yayin Gudanar da Taron Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai Gabatar da Takarda ta kasa da ke nuna Muhimmancin Najeriya wajen magance sauyin yanayi ta hanyar aiwatar da manufofin da aka tsara a cikin Ƙasar. Ya kuma yi amfani da damar da za ta faɗakar da shirye-shiryen Najeriya don yin aiki tare da abokan tarayya na kasashen waje don kawar da mummunar tasirin canjin yanayi a Afirka da kuma duniya baki daya.
A Yayin Ziyarar ta Shugaba Buhari kasar ta Poland, Shugaba Buhari zai yi ganawa ta Musamman da Shugaban kasar na Poland Andrdez Duda, da kuma Firayiministan Kasar Mateusz Morawiecki. Har ila yau, Shugaba Buhari zai Gana da ‘yan Asalin Najeriya mazauna kasar ta Poland Kafin ya dawo Gida Najeriya.
A Yayin Tafiyar Shugaba Buhari zai samu Rakiyar Gwamnonin Guda 3 da suka hada da Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na Jihar Enugu, sai Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello da kuma Takwaransa Na Jihar Naija Abubakar Sani Bello. Sauran a cikin ‘yan Tawagar sun hada da Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, Ministan Albarkatun Ruwa Mal. Suleiman Adamu, sai Ministan Harkokin Kiwon Lafiya, Ibrahim Jibrin.

No comments

Powered by Blogger.